
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya soke ziyarar aikin da ya shirya zuwa Kaduna inda zai ziyarci jihar Benuwe domin jajanta wa al’ummar jihar sakamakon munanan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar sama da mutum 100.
Shugaban zai kai ziyarar ne ranar Laraba domin duba halin da jihar ke ciki tare da nuna alhini da jajantawa a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga.
A lokacin ziyarar, shugaban ƙasar zai gana da manyan masu ruwa da tsaki na jihar, ciki har da sarakunan gargajiya da ‘yan siyasa da shugabannin addinai da kungiyoyin matasa da kuma sauran jagororin al’umma da nufin lalubo hanyoyin kawo ƙarshen rikicin.
Tun kafin ziyarar, shugaban ƙasa ya aike da tawagar wakilan gwamnatin tarayya zuwa jihar a ranar Litinin.
Tawagar ta ƙunshi Sakataren Gwamnatin Tarayya da Babban Sufeton ‘Yansanda da Shugabannin Hukumomin Leken asiri Da Tsaro da kuma Manyan Mambobin Kwamitocin Tsaro Na Majalisar Dokoki.
Hare-haren da aka kai a ƙarshen makon da ya gabata sun girgiza al’umma da dama, inda ake ci gaba da kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa wajen dakile ta’addanci a yankin.