Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2026 a gaban zaman hadin gwiwar Majalisar Tarayya gobe Juma’a da karfe biyu na rana.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ofishin Magatakardar Majalisar Tarayya ya fitar a jiya.
Sanarwar ta bukaci dukkan mutanen da aka tantance su halarci zaman majalisar tun daga karfe goma sha daya na safe, bisa dalilan tsaro.
Sanarwar ta kara da cewa daga wannan lokaci ne za a takaita shiga harabar majalisar.
A cewar bayanan da ke cikin Tsarin Kashe Kudi na Matsakaicin Lokaci na shekarun 2026 zuwa 2028, ana hasashen kasafin kudin shekarar 2026 zai kai kimanin naira tiriliyan 54.4.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa kudirin kasafin kudin na da nufin kawo karshen tsarin tafiyar da kasafin kudi fiye da guda a lokaci guda, tare da tabbatar da aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a fadin kasar nan.
Ya kara da cewa kudirin zai samar da tsari na gaskiya da bin doka wajen amincewa da kashe kudade, musamman a lokutan gaggawa, kalubalen tsaro da sauran muhimman bukatun kasa.
