Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da manyan hafsoshin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Villa.
Manyan hafsoshin sun isa fadar shugaban ƙasar da maraicen Talata, inda suka gana da shugaban har na tsawon sa’o’i uku.
Babu wani Karin bayani kan dalilan ganawar, ko kuma wasu daga cikin abubuwan da aka cimma yayin ganawar
Manazarta al’amuran kasa na ganin ganawar ba zai rasa nasaba da matsalar tsaron da ƙasar nan ke fuskanta.
Ganawar tasu na zuwa ne sa’o’i bayan Tinubu ya sanar da naɗin tsohon babban hafsan tsaro, Christopher G. Musa a matsayin ministan tsaro bayan saukar Badaru Abubakar.
