
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a wani taro na sirri da aka gudanar da daren Laraba a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke shirin gudanar da babban taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da aka tsara za a yi da ƙarfe 2 na rana yau Alhamis.
Rahotanni sun nuna cewa taron ya fara da misalin ƙarfe 7 na yamma, karkashin jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC (PGF), Sanata Hope Uzodimma na jihar Imo, tare da halartar dukan gwamnonin jam’iyyar.
Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa taron na da nufin tsara dabaru da shirye-shiryen cikin gida gabanin taron NEC, musamman batun maye gurbin tsohon shugaban jam’iyya na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi murabus .
Ana kallon wannan ganawa da taron NEC a matsayin wani mataki na sake daidaita tsarin jam’iyyar da kuma shiryawa babban zaɓen 2027 cikin ƙarfi da haɗin kai.