Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nanata cewa jami’an ‘yan sanda za su janye daga gadon manyan mutane a Najeriya, inda ya ce wannan mataki ya zama tilas.
A yayin taron majalisar zartarwa na ƙasa, Tinubu ya yi gargaɗin ɗaukar mataki kan duk wanda ya saba wannan umarni, tare da jaddada cewa babu ja da baya a aiwatar da shi.
Shugaban ƙasa ya bukaci Mai Ba Shi Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, Ministan ‘Yan Sanda Ibrahim Geidam, da Babban Sifeton ‘Yan Sanda na Ƙasa Kayode Egebtokun su tabbatar an aiwatar da wannan umarni ba tare da jinkiri ba.
Tinubu ya kuma bayyana cewa, bada kariya ga manyan mutane ba aikin ‘yan sanda ba ne, inda ya ce Ministan Harkokin Cikin Gida zai tsara yadda jami’an ‘yan sanda da ke gadon manyan mutane za a maye gurbinsu da jami’an Civil Defence.
