Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar Super Eagles murnar lashe lambar tagulla a gasar AFCON ta 2025 da aka gudanar a Morocco.
Shugaban ya bayyana nasarar a matsayin “tagulla mai ɗanɗanon zinariya,” yana yabawa juriyar da jajircewar ’yan wasan.
Super Eagles sun doke Masar, wadda ta lashe AFCON sau bakwai, ta bugun fanareti bayan wasan ya tashi kunnen doki.
Tinubu ya ce duk da rashin nasara a wasan kusa da na ƙarshe da Morocco, ’yan wasan sun nuna ƙarfin gwiwa da ruhin Najeriya.
Ya ce ’yan Najeriya za su yi alfahari da tawagar yayin karɓar lambar tagulla a Rabat, Morocco.
