Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da rage farashin wankin ƙoda daga Naira 50,000 zuwa Naira 12,000 ga marasa lafiyan da ke fama da cutar a faɗin ƙasar.
Guda daga cikin masu magana da yawun shugaban ƙasar, Daniel Bwala ne ya bayyana wannan mataki a shafinsa na X a jiya Litinin.
Ci gaban, wanda zai fara aiki a asibitocin gwamnati 10 na ƙasar, zai taimaka matuƙa ga dubban ‘yan Najeriya da ke fama da matsalolin ƙoda, wanda mafi yawansu basa iya biyan kuɗin wankin.
A cewar Mr Bwala, an ƙaddamar da fara aikin ragin kuɗin a fitattun asibitocin gwamnatin tarayya da ke shiyyoyi shida na ƙasar, kuma tuni wasu daga cikin marasa lafiyar da suka fara amfana suka bayyana jinɗaɗinsu a kai.
Asibitocin sun haɗa da asibitin tarayya na Ebute-Metta dake jihar Legas, da na Jabi dake Abuja, sai na Ibadan, da Owerri da kuma asibitin koyarwa na Maiduguri.
Sauran sun haɗa da na Abeokuta, da asibitin koyarwa na jihar Legas, da asibitin tarayyya na Azare, da na Benin da kuma Calabar.
Gwamnatin ta ce za’a ƙaddamar da shirin a ƙarin wasu asibitocin koyarwar da cibiyoyin lafiya na gwamnatin tarayya kafin ƙarewar wannan shekara, domin faɗaɗa shirin a faɗin ƙasar.
Masana lafiya na ganin wannan mataki a matsayin gagarumin ci gaba ga fannin lafiyar ƙasar, ganin yadda masu fama da ciwon ƙoda ke fama da biyan kuɗaɗen magunguna da wankinta, baya ga kalar abinci da ake shawartarsu su riƙa ci, wanda mafi yawansu basa iya cimma waɗannan ƙa’idoji, abinda ke kai ga asarar rayukan da dama.
