Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da sabon barikin sojoji da aka gina a Asokoro, Abuja.
Gwamnatin ta yi hakan ne don rage matsalar karancin matsuguni ga hafsoshin rundunar sojin.
Sabon barikin, wanda aka sanya wa suna “Bola Ahmed Tinubu Barracks”, na da wuraren zama ga manyan hafsoshi da jami’an soji na Janar-Janar 16 da Brigadier Janar 34 da Manjo-Kanal 60, Laftanar 60 da Manyan Hafsoshi 180 da kuma Kofur-kofur 264.
A barikin da akwai wuraren ibada da filayen wasanni da sauran abubuwan more rayuwa.
Barikin na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Tinubu na inganta jin daɗin jami’an tsaro da kara musu kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.