Shugaban kasa Bola Tinubu ya buƙaci, jami’an tsaron ƙasar su killace dazukan jihohin Kwara da Kebbi da kuma Neja, inda a baya-bayan nan ake samun ƙaruwar hare-hare tare da garkuwa da mutane.
Cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya buƙaci rundunar sojin saman ƙasar ta faɗaɗa sanya idanu ta sama kan dazukan, waɗanda ya yi imanin cewa nan ne mafakar yanbindigar.
Shugaba Tinubu ya buƙaci sojojin saman su faɗaɗa tsaron dazukan domin taimaka wa dakarun ƙasa.
A baya-bayan nan ne dai an samu garkuwa da ɗaliban a jihohin Kebbi da Neja da masu ibada a jihar Kwara
