Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da kafa wani asusu na musamman domin tallafa wa jami’an rundunar sojin Najeriya.
Yayin bikin cika shekaru 74 da haihuwarsa, Tinubu ya ce cikin waɗanda za su amfana har da waɗanda suka jikkata da kuma iyalan waɗanda suka rasu a bakin aiki.
A wata sanarwa da ya fitar, shugaban ya ce ya umarci babban akanta na ƙasa da ya buɗe wani asusu na musamman domin wannan shiri.
Tinubu ya kuma bayyana cewa zai bayar da dukkan albashinsa tun daga lokacin da ya hau mulki a matsayin tallafin farko ga asusun.
Ya ce, “A matsayin ƙuduri na kaina, zan zuba duk albashina tun daga lokacin da na karɓi mulki cikin wannan asusu domin fara shi.”
Shugaban ya yi kira ga gwamnoni, yan majalisar dokoki, yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki da su mara wa wannan shiri baya.
Ya jaddada muhimmancin girmama sadaukarwar jami’an tsaro, yana mai cewa wajibi ne a kula da su da iyalansu, ba sadaka ba ce illa hakki ne na ƙasa.
