
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin tarayya Abuja domin halartar taron shugabannin ƙasashe na Aqaba Process a birnin Rome na ƙasar Italiya.
Taron, wanda zai fara a ranar 14 ga watan Oktoba da muke ciki, zai mayar da hankali kan matsalolin tsaro da suka addabi yankin Yammacin Afirka.
An kaddamar da Aqaba Process ne a shekarar 2015 karkashin jagorancin Sarkin Jordan, Abdullah II, tare da haɗin gwiwar gwamnatin Italiya, inda Manufarsa ita ce ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashe da hukumomin tsaro wajen yaki da ta’addanci da sauran manyan barazanar tsaro.
A cewar fadar shugaban ƙasa, tattaunawar za ta mayar da hankali kan yadda za’a magance yaɗuwar ƙungiyoyin ta’addanci a yankin Sahel, da haɗin gwiwar da masu laifi ke yi da ‘yan ta’adda, da kuma barazanar ta’addanci da fashi a teku da ke ƙara taɓarɓarewa a Tekun Guinea.
Za’a kuma tattauna yadda za’a yaki yaɗa ra’ayin ƙungiyoyin ta’addanci a intanet da kuma yadda za’a katse hanyoyin sadarwar da suke amfani da su wajen yaɗa saƙonni da kuma jan magoya baya.