
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da aikin titin kilomita 100 na Legas zuwa Kalaba, wanda zai ratsa ta Jihar Edo.
Ministan Ayyuka, Dave Umahi ne ya sanar da haka a yayin sanya ido akan wani ɓangaren aikin tagwayen titin Benin zuwa Warri na Edo da ba a ƙarasa ba, a ranar Alhamis.
Da yake tsokaci akan halin rashin kyawun hanyar, Ministan ya ce babu wani mai abin hawa da zai yi tuƙi har na tsawon kilomita 100 a titunan gwamnatin tarayya ba tare da fuskantar ƙalubalen lalacewar wasu wurare ba, yana mai cewa hakan abu ne da shugaban ƙasar ya gada daga ayyukan da gwamnatocin baya suka bayar.
Ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu kan yadda ya nuna damuwa game da al’amarin da amincewa da cigaba da ayyukan don amfanin al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.
Umahi ya ƙara da cewa amince wa aikin da Tinubu ya yi sakamakon biyayya, shugabanci da ƙoƙarin sauke nauyin jagorancin.