
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da ci gaba da aikin haƙar man fetur na Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.
Ministan albarkatun mai na Najeriya, Heineken Lokpobiri ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Nneamaka Okafo ya fitar ranar Lahadi.
Ministan ya ce, tuni gwamnatin Tarayya ta samar da wata cibiyar nazarin albarkaun man fetur da iskar gas a ƙaramar hukumar Alƙaleri da ke jihar Bachi domin tabbatar da an samu nasarar ɗorewar ci gaba da aikin.
A watan Nuwamban 2022 ne aka fara aikin shirin haƙar mai na Kolmani, wanda ya bayar da damar soma neman ɗanyen man a shiyar arewacin Najeriya, wanda yanki ne na kogin Kolmani mai tarin arzikin man da ke tsakanin jahohin na Bauchi da Gombe.
A makon da ya gabata shugaban kamfanin haƙar man fetur na ƙasa, Bayo Ojulari ya ce kamfanin NNPCL ɗin zai ci gaba da aikin tono man a rijiyar ta Kolmani.