Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar tabbatar da adalci a sha’anin haraji da shugabanci a nan Kano (Tax Justice & Governance Platform) ta baiwa kugiyoyin al’umma horo kan ilimin kasafin kudi da bibiyar harajin da gwamnati take karba.
An bayar da horon a ranakun Talata da Laraba domin ilimantar da kungiyoyin hanyoyin da zasu samar da sauyi ga tsarin aiyuka da ake sanyawa cikin kasafin kudi da bibiyar yadda ake amfani da harajin da suke biya.
Jami’I mai kula da shirye-shiryen kungiyar Sadiq Muhammad Mustapha, ya ce a baya sun fito da tsarin wayar da kan masu biyan haraji musamman wadanda suke karkara kan damar da suke da ita na bayyana irin abubuwan da suke so ayi musu da harajin da suke biya.
Ya ce horon da aka basu zai taimaka musu ta hanyar bayyanawa gwamnati irin aiyukan da suke so a sanya musu cikin kasafin kudi.
Ya ce zai kuma taimaka musu wajen bibiyar aiyuka da kudin da aka fitar da tabbatar da cewa an yi musu aiyukan da aka sanya a kasafin kudi.
Sadiq Mustapha, ya kara da cewa kungiyoyi suna bayar da gudunmawa wajen tsara kasafin kudi amma da yawa basa bibiya su tabbatar ana aiwatar da aiyukan da aka sanya.
A nata bangaren matemakiyar darakta a hukumar wayar da kai ta kasa NOA a nan Kano, Grace Musa, ta ce taron zai taimaka wajen kawo sauyi a shanin yadda gwamnatoci ke aiwatar da aiyuka.
Ta ce zasu fadada irin wannan horo ga sauran kanannan hukumomi dake fadin jihar Kano.
Shi kuwa Kwamaret Abbas Ibrahim da ya wakilci shugaban kungiyar kwadago reshen Kano, kwamaret Kabiru Inuwa, ya ce horon da aka bayar zai taimaka wajen gano inda hakkin al’umma yake tare da neman gyara.
Da yake jawabi Garba Bello daga ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Kano, ya ce doka ta baiwa kowane dan kasa damar bibiya da neman bayani kan abubuwan da gwamnati ke aiwatarwa.
Ya bukaci kungiyoyin al’umma da ‘yan jarida su hada kai wajen bibiyar kasafin kudi da aiyukan da aka sanya a ciki.
Taron na kwanaki biyu da kungiyar Tax Justice & Governance Platform ya samu halartar kungiyoyi, jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki daga bangarori daban daban.
