
Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaba da kashi 3.13 cikin 100 a watanni uku na farkon shekarar 2025.
Wannan ya ninka ƙimar kashi 2.27 cikin 100 da aka samu a cikin lokaci iri ɗaya a shekarar 2024.
A cewar rahoton da hukumar ta fitar ranar Litinin, ɓangarorin da suka fi taka rawa wajen haɓaka tattalin arziƙin sun haɗa da sashen ayyuka, masana’antu, noman ƙasa da kasuwanci, kamfanonin sadarwa, da kuma man fetur da iskar gas.
Shugaban hukumar, Adeyemi Adeniran, ya sanar da sabunta kididdigar GDP daga shekarar 2019, inda sabon adadin ya kai naira tiriliyan 205, ƙaruwa da kashi 41.7 cikin 100 idan aka kwatanta da rahoton shekarar 2014.
Adeniran ya ce sabunta bayanan zai ba da damar ingantaccen tsare-tsare na tattalin arziki da kuma fahimtar ainihin rawar da kowane ɓangare ke takawa a bunkasar ƙasa.