Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa talauci shi ne babban tushen matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar Arewacin Najeriya.
Gwamnan ya yi wannan furuci ne a Kaduna, yayin bikin cika shekaru 25 da kafuwar Kungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) tare da kaddamar da Asusun Tallafin kungiyar, kamar yadda kakakinsa, Hamisu Mohammed Gumel, ya bayyana a wata sanarwa.
Namadi ya ce duk da cewa matsalolin tsaro suna kara ta’azzara a yankin, wajibi ne a duba tushen matsalar domin samar da ingantaccen mafita. Ya ce talauci, rashin wadataccen tattalin arziki, da karancin damammakin aiki su ne manyan dalilan da ke haifar da rashin tsaro.
Gwamnan ya jaddada cewa Arewacin Najeriya na da albarkatu masu tarin yawa, musamman filayen noma, ƙarfafa a fannin samar da ma’aikata, da sauran damar cigaba, wadanda idan aka yi amfani da su yadda ya kamata, za su taimaka wajen rage talauci da inganta tsaro a yankin.
Ya kuma bukaci cibiyoyi, gwamnati da kuma kungiyoyin Arewa da su mayar da hankali wajen aiwatar da tsare-tsaren da za su inganta rayuwar al’umma domin magance matsalolin tsaro daga tushe.
