Kamfanin Dangote zai samar da takin zamani tan 16,940 na uriya tare da hadin gwiwar kamfanin thyssenkrupp Uhde dake ƙasar Jamus
Katafaren kamfanin Dangote bangarensa dake samar da takin zamani zai gudanar da aikin ne a wasu sabbin cibiyoyin da zai samar guda hudu a Najeriya.
Sanarwar hakan ya fito daga kamfanin ne bayan da bangarorin biyu suka rattaɓa hannu a kan yarjejeniyar aiki tare da samar da lasisi da kuma na’urorin aiki, ciki har da manyan injinan sarrafa takin.
- Gwamnatin tarayya ta sasanta rikicin PENGASSAN da matatar man Dangote
- Matatar Dangote Za Ta Gina Runbum Ajiye Mai A Namibia
“Kowanne sashe na kamfanonin guda hudu zai iya samar da tan 4,235 na takin a kowacce rana, abin da zai bunƙasa takin yuriyar da kamfanin ke sarrafa daga tan miliyan 2,650,000 zuwa tan miliyan 8.
“Za’a gina waɗannan wuraren sarrafa takin ne a unguwar Lekki dake Lagos, kusa da kamfanin Dangoten dake samar da taki tan 3,850 kowacce rana tun daga shekarar 2021”. In ji sanarwar.
Kamfanin ya kuma ce, sabbin wuraren samar da takin da za’a yi za su taikaita fitar da ƙurar dake gurbata muhalli kamar yadda hukumomi ke buƙata.
Majalisar Dattawan ta yi watsi da babban kamfanin mai na ƙasa NNPCL game da bacewar kudi naira tiriliyan 210
