Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce matsalar tsaro a yankin Arewa na damunsa matuƙa saboda tana kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban Najeriya.
Ya bayyana haka ne a Jihar Kaduna, yayin bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), wanda Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya wakilce shi.
Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta gaji matsalolin tsaro masu yawan gaske, amma tana aiki tuƙuru don magance su.
Ya yi gargaɗin cewa Najeriya ba za ta ci gaba ba idan al’ummarta suka ci gaba da fuskantar hare-hare, talauci, da tsoro.
Shugaban Ya yi kira ga shugabannin Arewa da su zama masu gaskiya da jarumta wajen nemo mafita.
Ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta kawo ƙarshen ’yan ta’adda da ’yan fashi, tare da farfaɗo da tattalin arziƙin yankin.
Tinubu ya ce yana fatan ganin Arewa mai aminci, ciki har da samar da man fetur daga yankunan Arewa da manyan ayyuka kamar sabon titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
Ayayyin taron dai Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu, ya yi Allah-wadai da kashe-kashe da garkuwa da ɗalibai da malamai a jihohin Neja da Kebbi.
Ya roƙi gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa don kawo ƙarshen tashin hankali.
