Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon shugaban rundunar sojin ƙasa kuma tsohon Ministan Kula Da Al’amuran Cikin Gida, Janar Abdulrahman Dambazau a matsayin jakadan Najeriya #Tinubu.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar sabbin naɗe-naɗen jakadun a gaban majalisar a yayin zamanta na ranar Alhamis.
Sauran mutanen da Tinubu ya kuma naɗa a matsayin jakadun sun hada Tsohon shugaban rundunar sojin ruwa kuma tsohon Kantoman jihar Ribas, Ibok-Ete Ekwe Ibas da Ita Enang, tsohon sanata da uwargidan tsohon gwamnan jihar Imo Chioma Ohakim da tsohon ministan cikin gida kuma #Tinubu.
Mika sunayensu ga majalisar na zuwa ne ’yan kwanaki bayan da shugaba Tinbu ya aike wa Majalisar jerin farko na waɗanda yake son nadawa a matsayin jakadun.
A cikin wasikar, shugaban ƙasa ya roƙi ’yan majalisa da su yi gaggawar duba sunayen domin bai wa gwamnati damar cike muhimman guraben jakadun.
Dan asalin jihar Kano, an haifi Janar Dambazau a ranar 14 ga watan Maris na shekara ta 1954, ya kuma rike mukamai dadan-daban a rundunar sojin kasarnan kafin ya yi ritaya a matsayin Babban Hafsa kuma Shugaban Ma’aikatan Sojoji daga shekara ta 2008 zuwa 2010.
Ya kuma Ministan Kula da Al’muran cikin gida daga shekara ta 2015 zuwa 2019. A halin yanzu shi ne shugaban Jami’ar Capital City mai zaman kanta a Kano .
