Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya ce sukar da al’umma ke yi kan yawaitar tafiye-tafiye da gwamnoni ke yi, na yin hakan ne saboda rashin fahimtar yadda aikin gwamnati ke gudana.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai, inda ya ce ya lura da yadda wasu ’yan kasa ke yawan yin korafi kan tafiye-tafiye da gwamnonin ke yi, yana mai cewa da dama na kallon duk wata tafiyar gwamna a matsayin hutawa ko yawon shakatawa.
A cewarsa, a mafi yawan lokuta, irin wadannan tafiye-tafiye na da alaka kai tsaye da neman hanyoyin bunƙasa ci gaba, jawo zuba jari da kuma samar da ayyukan alheri ga al’ummar jiha.
Gwamnan ya kara da cewa sakamakon irin wadannan tafiye-tafiye ne ake samun damar cimma muhimman manufofin raya kasa da kuma inganta jin dadin al’umma.
Kalaman gwamnan na zuwa ne a yayin da yake mayar da martani ga sukar da wasu ke yi masa dangane da yawaitar tafiye-tafiye a cikin da wajen jihar Katsina.
