
Shugaban 'yan tawayen Sudan Janar Dagalo da aka fi sani da Hametdi
Kungiyar RSF da sojojin Sudan ta fatattaka daga Khartoum ta ce tsugune bai kare ba, domin za ta ci gaba da yaki a kasar
Shugaban kungiyar Janar Dagalo ne ya fadi haka a jawabinsa na farko tun bayan da sojojin gwamnati suka fatattaki kungiyarsa daga babban birnin kasar Khartoum.
Ya kuma fadi haka ne a cikin wani sakon sauti na Telegram yana mai cewa RSF ta yanke shawara ta dabara ta barin Khartoum, don “sakewa a Omdurman”, tagwayen birnin Khartoum da RSF ta yi amfani da ita a baya wajen kai hare-hare.
Rahotanni na cewa, RSF ce ke rike da wasu yankunan Omdurman, wanda galibin sojoji kungiyar ke iko da su, a makon da gabata kungiyar ta ce ta karbe ikon Souq Libya, wata babbar kasuwa a yammacin Omdurman, kuma daya daga cikin muhimman cibiyoyin kasuwanci a Sudan.
Rugujewar Sulhu
Bangarorin sun yi watsi da batun sulhu a tsakaninsu inda ka rawaito shugaban RSF na cewa “babu wata tattaunawa da sojojin gwamnati, ya kuma kira tattaunawar “motsi na yaudara. Ba mu da wata yarjejeniya ko tattaunawa da su. Harshenmu makamai kawai. in ji shi.”
An kuma rawaito babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da yin watsi da duk wani sulhu da kungiyar ta RSF, yana mai shan alwashin murkushe ta.
“Ba za mu yafe ba, ba za mu yi sulhu ba, ba za mu tattauna ba,” in ji shi,
Shugaban yana mai jaddada aniyar sojojin kasar da maido da da hadin kan kasa da zaman lafiya.
Rikicin mulki na tsawon shekaru biyu tsakanin bangarorin biyu gabanin komawa mulkin farar hula a kasar ya lalata mafi yawan Khartoum babban birnin kasar, tare da raba sama da mutane miliyan 12 da muhallinsu, lamarin da ya kai ga abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira rikicin jin kai mafi muni a duniya, a inda rabin kasar ke fama da matsananciyar yunwa.