Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano tare da hadin gwiwar Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, wato UNICEF, sun shirya bita ta kwana biyu domin horas da Jami’an Duba Makarantu saba’in daga kananan hukumomi goma na jihar.
Taron bitar na gudana ne a dakin taro na SBMC da ke hedikwatar hukumar, inda ake koyar da sabbin dabaru na inganta aikin duba makarantu, da kuma tabbatar da ingantaccen tsarin koyo da koyarwa a Matakin farko.
Da yake bude taron, Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano, Malam Yusuf Kabir, wanda ya samu wakilcin Daraktan Ayyuka na Musamman, Malam Nura Ibrahim, ya bayyana cewa manufar bitar ita ce kara wa jami’an duba makarantu kwarewa karkashin shirin Foundational Learning (FLN), wanda ake koyar da shi cikin harshen Hausa bisa tsarin rana.
Ya ce horon zai taimaka wajen ba jami’an duba makarantu sabbin dabaru da zasu inganta aikinsu, tare da tallafawa malamai wajen shawo kan matsalolin da ke hana ingantaccen koyo da koyarwa a makarantu.
Malam Nura ya bukaci jami’an da su mayar da hankali kan abin da ake koyarwa, tare da gudanar da aikinsu cikin gaskiya da amana. Ya kuma shawarce su da su rika bayar da rahotanni akan lokaci, domin a sami nasarar shirye-shiryen cigaban ilimi a fadin jihar Kano.
Ya kara da cewa wannan bita na daya daga cikin muhimman shirye-shiryen hadin gwiwar SUBEB da UNICEF, domin tabbatar da cewa yara a Kano suna samun ilimi mai inganci tun daga tushe.
Shi ma daya daga cikin masu bayar da horon, Dr. Bala Dambatta, ya bayyana cewa shirin na UNICEF zai kara karfafa tsarin koyo da koyarwa a makarantun firamare.
Ya ce a baya ana bai wa malamai horo ne kawai, amma shigar da jami’an duba makarantu cikin tsarin zai kara tabbatar da kulawa da inganta aikin koyarwa kai tsaye.
Wasu daga cikin jami’an da suka halarci bitar sun bayyana farin cikinsu da wannan horo, inda suka sha alwashin aiwatar da sabbin dabarun da suka koya a makarantu, tare da rika bayar da rahotanni akai-akai domin tabbatar da ci gaba a fannin ilimi.
Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano tare da hadin gwiwar Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, wato UNICEF, sun shirya bita ta kwana biyu domin horas da Jami’an Duba Makarantu saba’in daga kananan hukumomi goma na jihar.
Taron bitar na gudana ne a dakin taro na SBMC da ke hedikwatar hukumar, inda ake koyar da sabbin dabaru na inganta aikin duba makarantu, da kuma tabbatar da ingantaccen tsarin koyo da koyarwa a Matakin farko.
Da yake bude taron, Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano, Malam Yusuf Kabir, wanda ya samu wakilcin Daraktan Ayyuka na Musamman, Malam Nura Ibrahim, ya bayyana cewa manufar bitar ita ce kara wa jami’an duba makarantu kwarewa karkashin shirin Foundational Learning (FLN), wanda ake koyar da shi cikin harshen Hausa bisa tsarin RANA.
Ya ce horon zai taimaka wajen ba jami’an duba makarantu sabbin dabaru da zasu inganta aikinsu, tare da tallafawa malamai wajen shawo kan matsalolin da ke hana ingantaccen koyo da koyarwa a makarantu.
Malam Nura ya bukaci jami’an da su mayar da hankali kan abin da ake koyarwa, tare da gudanar da aikinsu cikin gaskiya da amana. Ya kuma shawarce su da su rika bayar da rahotanni akan lokaci, domin a sami nasarar shirye-shiryen cigaban ilimi a fadin jihar Kano.
Ya kara da cewa wannan bita na daya daga cikin muhimman shirye-shiryen hadin gwiwar SUBEB da UNICEF, domin tabbatar da cewa yara a Kano suna samun ilimi mai inganci tun daga tushe.
Shi ma daya daga cikin masu bayar da horon, Dr. Bala Dambatta, ya bayyana cewa shirin na UNICEF zai kara karfafa tsarin koyo da koyarwa a makarantun firamare. Ya ce a baya ana bai wa malamai horo ne kawai, amma shigar da jami’an duba makarantu cikin tsarin zai kara tabbatar da kulawa da inganta aikin koyarwa kai tsaye.