
Shugaban Majalisar Mulkin Sudan, Abdel Fattah al Burhan, ya ce sojojin kasar sun shirya tattaunawa don kawo ƙarshen yaƙi da dawo da haɗin kai da martabar Sudan.
Yayin da yake magana a Atbara da ke arewacin Sudan jiya Asabar Burhan ya bayyana cewa babu wata tattaunawa da ake yi a halin yanzu da ƙasashe huɗu (Amurka, Saudiyya, Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa) ko wata ƙungiya daban.
Burhan ya jaddada cewa rundunar sojojin ƙasar “za ta ci gaba da yaƙar abokan gaba duk inda aka same su” kuma ya musanta zargin cewa suna kai hari kan ƙabilu ko yankuna.
Ya ce waɗanda suke neman zaman lafiya da gaske suna maraba da su, amma “tilasta zaman lafiya ko kafa gwamnati kan mutane ba tare da yardarsu ba abin ƙi ne.”
Waɗannan kalaman nasa sun zo ne kafin tarukan da ƙasashe huɗu suka shirya yi a birnin New York don ƙoƙarin samar da mafita mai dorewa ga yaƙin Sudan