Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta na kasa da kasa (MNJTF) sun yi nasarar daƙile wani hari na taron dangi na ‘yan ta’addan Boko Haram kan sansanin soji da ke Darak a ƙasar Kamaru.
A cewar wata sanarwar da Babban Jami’in Yaɗa Labaran Soji rundunar, Laftanar – kanar Olaniyi Osoba ya fitar a ranar Alhamis, an kai musu harin ne da sanyin safiyar ranar Laraba.
Yayin harin, ‘yan ta’addan sun kai farmaki daga wurare da dama a sansanin.
Bayan artabu sojojin sun harbe mutum Shida wanda hakan ya tilasta wa sauran guduwa da raunuka daban-daban na harbin bindiga.
“Sai dai wasu sojoji biyar sun samu raunuka wanda a halin yanzu suke samun kulawa a asibiti”. Inji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, sojojin sun kai wani samame na bin baya kan ‘yan ta’addan da suka tsere a ƙauyen Mazogo da ke tsakanin Zamba da Djibirilli.
Sojin sun yi nasarar harbe ‘yan ta’addan huɗu, sun kuma samu nasarar ƙwato wasu kayayyakin maharani har da abinci.