Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya da fararen hula a gabashin Kongo sun tsere zuwa Rwanda, bayan sojojin Kongo sun “miƙa wuya” ga jami’an tsaron Rwanda.
Hakan ya biyo bayan ‘yan tawayen M23 sun ƙwace birnin Goma.
Bidiyoyi da gidan Radiyo da Talabijin na Rwanda suka wallafa a shafin X sun nuna sojojin Kongo suna miƙa makamai ga jami’an tsaron Rwanda, bayan tsallakawa zuwa iyakar ƙasar a yankin Rubavu na Rwanda.
Lamarin ya faru ne sa’o’i bayan ‘yan tawayen M23 sun bayyana cewa sun shiga Goma, wanda ya tilasta wa al’ummar birnin neman tsira daga cikin garin.
‘Yan tawayen, wadanda ake zargin suna samun goyon bayan Rwanda, sun ƙara yin ƙoƙari wajen kulla iko a gabashin Kongo, tare da kwace wasu birane a makon jiya.
Sai dai, Shugaban Rwanda Paul Kagame ya musanta duk wani zargi na goyon baya ga ‘yan tawayen M23.
Haka zalika, an fuskanci wani gagarumin fasa gidan yari a birnin Goma a safiyar Litinin, bayan da ‘yan tawayen M23 suka shiga birnin, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa AFP.
