Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da cewa dakarunta za su ci gaba da zama a wasu muhimman wurare biyar a Lebanon daga ranar Talata, matakin da ya saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta da Hezbollah.
A karkashin yarjejeniyar, sojojin Lebanon za su koma kudancin kasar tare da dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD, yayin da sojojin Isra’ila suka janye na tsawon kwanaki 60, wanda aka tsawaita har zuwa 18 ga watan Fabrairu.
Kakakin rundunar sojin Isra’ila, Laftanar Kanar Nadav Shoshani, ya bayyana cewa sun yi hakan ne domin kare lafiyar al’umma da kuma tabbatar da babu barazana.
Ya kuma ce, za a bar wasu kananan dakaru na wucin gadi a wurare guda biyar a iyakar Lebanon.
