Yawan sojojin Isra’ila dake kashe kawunansu na karuwa a wata sanarwar da Rundunar sojin kasar ta fitar.
Sojojin Isra’ila 28 ne suka kashe kansu tun da kasar ta kaddamar da yaki a Gaza, kari kan na shekarar 2024.
Wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar ta ce, an yi hasashen sojoji 17 ne suka “kashe kawunansu” a shekarar 2024.
“Wadannan alkaluma sun zarta na shekarar 2023 inda sojojin kasar suka hallaka ‘kansu ciki har da guda bakwai da suka kashe kawunansu bayan soma yakin” in ji sanarwar.
A cewar TRT, sanarwar ba ta bayar da dalilin kashe kawunan na su ba, sai dai hakan ba zai rasa nasaba da abin masu sharhi kan al’amuran yau da kullun da cewa “alhakin Falasdinawan da ake zulunta ne”.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe sojojinta akalla 891 tare da jikkkata 5,569 tun bayan da aka soma yakin awayan Oktoban 2022.
Sanarwar ta ce an kashe sojoji 363 a shekarar 2024, da kuma sojoji 558 a 2023, sabanin sojoji 44 da aka kashe.
TRT ta rawaito cewa, Rundunar sojin Isra’ila ta bude layin tarho wanda zai yi aiki babu dare babu rana domin bayar da shawarwari na kula da lafiyar kwakwalwar sojin da cikin matsanacin damuwa.
Musamman ga sojojin da ke cikin damuwar da ka iya kai wa ga kisan Kai, “sannan an kara ma’aikata da ke lura da lafiyar kwakwalwa domin hana masu son kashe kawunansu.” Inji sanarwar.
Kamfanin yadda labaran na Turkiyya ya kuma rawaito cewa, Duk da kudurin da Kwamitin Tsaro na MDD ya yi wanda ya yi kira ga Isra’ila ta dakatar da bude wuta a Gaza, amma hakan ya faskara.
Rundunar sojin Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare na kisan kiyashi da suka kashe Falasɗinawa fiye da 45,600, galibinsu mata da yara, tun daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023.
A watan Nuwamban 2024, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta bayar da umarnin kama firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan Tsaron ƙasar Yoav Gallant bisa aikata laifukan yaki.