
Rundunar sojin Najeriya ta ce, dakarunta na Operation HADIN KAI sun samu gagarumar nasara a dajin Sambisa, a inda suka hallaka mayaƙan Boko Haram da dama a wani samame da suka kai a yankin Lardin Buttu da ke jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X (tsohon Twitter), rundunar ta bayyana cewa harin ya gudana ne ranar 11 ga Mayu, inda sojojin suka yi arangama da ’yan ta’adda a cikin dajin, tare da kwato makamai da kayan yaƙi masu tarin yawa.
Kyaftin Reuben Kovangiya, mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar, ya tabbatar da cewa wannan nasarar babban ci gaba ne a fafutukar da ake yi wajen murkushe ƙungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.
Rundunar ta bayyana cewa yankin Ladin Buttu na daga cikin manyan sansanonin Boko Haram, inda ’yan ta’addan ke tsara hare-hare, da adana makamai da kayayyakin yaƙi.
Wannan samame na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da sabbin hare-haren ’yan Boko Haram a wasu sassan jihar Borno, lamarin da ya jaddada bukatar ci gaba da matsin lamba kan kungiyoyin ta’addanci.