
Dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar kashe wani babban kwamandan ƙungiyar Boko Haram ko ISWAP mai suna Ibn Khalid a wani artabu a ƙaramar hukumar Gwoza da ke jihar Borno.
Ibn Khalid, wanda aka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu tsara hare-haren ta’addanci da yaɗa bidiyon ƙungiyar ga mabiyanta a kafafen sada zumunta, ya rasa ransa yayin wani samame da dakarun Operation Hadin Kai suka kai a yankin Bitta.
A cewar mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Reuben Kovangiya, artabun ya gudana ne a lokacin da sojojin suka daƙile yunkurin mayakan ƙungiyar na kutsawa cikin garin.
Ya kuma bayyana cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama a artabun, ciki har da kwamandan da mai ɗaukar bidiyo na ƙungiyar.
“Sojojinmu sun kwato makamai da dama ciki har da bindigogi, harsasai, babura da kuma kyamarar ɗaukar bidiyo da ‘yan ta’addan ke amfani da ita wajen yaɗa hare-harensu.
“Dakarun sun daƙile wani hari da mayakan suka shirya kaiwa Monguno, tare da ci gaba da kai hare-hare cikin dajin Sambisa zuwa yankunan Madagali da Kaga”. In ji Kyaftin Kovangiya.
Kakakin ya kuma kara da cewa, an kashe ‘yan ta’adda 17 a waɗannan hare-haren, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato ƙarin makamai.