Rudunar sojin sama sun fatattaki mayaƙan Lakurawa daga wasu yankunan jihar Kebbi da Sokotoa bayan da suka yi musu luguden wuta.
Sojojin sun ragargaji Lakurawan ne kwanaki kaɗan bayan da mayaƙan na ƙasashen suka addabi yankin
Harin su baya-bayan nan shine wanda suka halaka mutane 17 suka kuma sace dabbobi a garin Mera ta karamar hukumar Augie.
Kakakin gwamnan Kebbi, Abdullahi Umar Zuru ya ce, bayan harin ne sojoji suka isa yankin,
“Sojojin sun kai ɗauki ne bayan roƙon da Gwamna Ahmad Idris ya yi na kawar su daga jihar, kuma aka samu nasarar fatattakarsu da kuma ƙwato dabbobin sata da dama”. Inji shi
A ranar Talata ne Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu a wani taro a Abuja ya bayar da tabbacin cewa jami’an tsaron kasar nan za su fatattaki ‘yan bindigan cikin lokacin kankani.