
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta bayyana nadamarta kan hallaka wasu ’yan bijilanti Ashirin a wani harin da jiragenta suka kai bisa kuskure a ƙaramar hukumar Maru, Jihar Zamfara.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar a yammacin Litinin, an bayyana cewa jiragen rundunar sun kai hari ne domin fatattakar ’yan bindiga da suka addabi yankin, amma cikin rashin sani suka halaka ’yan sa-kai da ke kokarin kare al’ummarsu.
“Mun samu rahoton gaggawa na wani harin ’yan bindiga a yankin, kuma a kokarin mu na kawo dauki cikin hanzari, an samu wannan kuskure da ya yi sanadiyyar rasa rayukan wasu daga cikin masu taimaka wa jami’an tsaro,” in ji sanarwar.
Rundunar ta ce, duk da wannan mummunan lamari, sojojin sun samu nasarar kashe ’yan bindiga 20 tare da kwato babura masu yawa da suka yi amfani da su wajen kai farmaki.
Sai dai mazauna yankin sun bayyana takaicinsu, inda suka ce sun riga sun sanar da jami’an tsaro bayani dalla-dalla game da harin da ’yan bindigar suka kai, ciki har da inda ’yan bijilanti ke kokarin dakile su.
“Mun kira jami’an tsaro tun farko, amma daga bisani kawai sai muka ga jirgin ya zo ya kashe ’yan sa-kai,” in ji wani mazaunin yankin da ya zanta da BBC.
Harin na baya-bayan nan na zuwa ne watanni kadan bayan wani mummunan harin jirgin soji da ya hallaka mutum 16 a ƙauyen Tungar Kara a cikin watan Janairu na wannan shekarar.
A wannan harin ma, an kashe ’yan sa-kai da manoma da ake zargin ’yan bindiga ne.