Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu umarci hukumomin tsaro da su kubutar da dalibai mata da ’yan bindiga suka sace.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
“Shugaban Ƙasa ya ba hukumomin tsaro umarnin kai tsaye da su gano inda daliban suke, su kuma kubutar da su cikin koshin lafiya, tare da tabbatar da cewa dukkan masu hannu a lamarin sun fuskanci hukunci”. In ji Ministan a sanarwar.
Ministan ya kuma yi kira ga ’yan kasa da su kwantar da hankali, tare da ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya a yayin da ake cigaba da kokarin ceto yaran.
Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da kai harin a Makarantar Sakandiren ’Yan Mata ta Maga, inda aka kashe mataimakin shugaban makarantar.
