
Shubgaban Hukumar JAMB Farfesa Oloyede ya fashe da kuka yayin da yake jawabi, yana mai bayyana takaicinsa kan wahalar da ɗalibai suka fuskanta sakamakon tangardar fasaha da aka samu da hakumar ta ta bayyana faduwar jarrabawar UTME ta bana.
Farfesan ya fashe da kukan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, inda ya nuna nadamarsa tare da bai wa ɗalibai haƙuri.
Hukumar JAMB ta bayyana cewa matsala a tsarin tattara bayanai ne ya haddasa mummunan sakamakon da dalibai da dama suka fuskanta a jarabawar UTME ta bana.
A cewarsa, dalibai 379,997 da lamarin ya shafa za su sake rubuta jarabawa, musamman a jihohin Kudu-Maso-Gabas da Jihar Legas.
Shuganban ya kuma ce, an riga an sanya sabuwar rana don sake jarabawar, kuma masu ruwa da tsaki za su fara karɓar saƙo daga hukumar daga ranar Alhamis.
Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka rubuta UTME ta bana, fiye da miliyan 1.5 sun kasa samun maki 200 daga cikin 400, abin da ya jawo damuwa a fagen ilimi da ce-ce-ku-ce daga iyaye da malamai.
Hukumar ta JAMB ta tabbatar da cewa tana daukar matakan gyara tare da tabbatar da gaskiya da adalci ga daliban da suka cancanta.