Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Laminu Rabiu, ya sanar da murabus ɗinsa daga shugabancin hukumar, inda ya danganta matakin da sauye-sauyen da ke faruwa a fagen siyasar jihar tare da buƙatar sake daidaita alkiblarsa.
Laminu Rabiu ya bayyana cewa murabus ɗinsa ya dogara ne kacokam kan biyayyarsa ga tafiyar Kwankwasiyya da kuma jagoranta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A cewarsa, matakin zai ba shi damar bayar da cikakkiyar gudunmawa wajen cimma manufofin tafiyar a wannan lokaci.
Murabus ɗin nasa na zuwa ne bayan wasu manyan jami’an gwamnatin jihar sun ajiye mukamansu a baya-bayan nan.
Daga cikin su akwai Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman, Air Vice Marshal Ibrahim Umaru (mai ritaya), da Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo, sai kuma Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso, waɗanda duk suka fice daga muƙamansu.
A gefe guda kuma, wasu daga cikin masu riƙe da muƙamai na ci gaba da bayyana goyon bayansu ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da daidaita matsayarsu da tafiyarsa ta siyasa.
Daga cikinsu akwai Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Masarautu, Farfesa Tijjani Muhammad Naniya, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.
Farfesa Tijjani Muhammad Naniya ya bayyana cewa matakin na sa na da nasaba da buƙatar daidaita matsayarsa ta siyasa da Gwamnan Jihar Kano.
Wannan na ƙunshe ne cikin wasiƙar murabus ɗin da ya aikawa Shugaban Jam’iyyar NNPP na Mazabar Bakin Ruwa a Ƙaramar Hukumar Dala.
