Shugaban Angola kuma shugaban Tarayyar Afirka (AU), ya gabatar da wasu shawarwari don kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.
Duk da cewa an bayyana shawarwarin a matsayin masu matuƙar ban sha’awa, ba a fitar da cikakkun bayanai ba.
Ofishin shugaban Angola ya bayyana cewa ya gana da shugaban Congo, Felix Tshisekedi, a Luanda na tsawon sa’o’i domin tattauna rikicin da ƙoƙarin kawo ƙarshen sa.
A nasa bangaren, Tshisekedi ya ce shawarwarin João Lourenco na iya “taimakawa matuƙa” wajen samun zaman lafiya a yankin.
Ganawar ta zo ne kwanaki kafin taron kwanaki uku da ministocin tsaro na ƙasashen tsakiya da gabashin Afirka za su yi a Zambia, domin tattauna halin tsaro a Congo.
Duk da yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka cimma a baya, sabon rikici ya ɓarke a ranar 3 ga Janairu tsakanin ƙungiyar M23, wadda ke samun goyon bayan Rwanda, da sojojin gwamnatin Congo.
