Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da sabbin hafsoshin tsaro a fadar gwamnatin tarayya a Abuja.
Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban ya gana da su bayan nadin su a farkon makon nan.
Babu wani karin bayani kan ganawar, amma wata majiya daga fadar ta ce, taron ba zai rasa nasaba da ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsaro da inganta aikin rundunar sojoji ba.
Waɗanda suka halarci taron akwai babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, da babban Hafsan Sojin Ƙasa, Manjo Janar Waheedi Shaibu, da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Vice Marshal Kennedy Aneke; da kuma Babban Hafsan Rundunar sojin Ruwa Rear Admiral Idi Abbas, da kuma Babban Daraktan Leken Asiri na Sojoji, Mejo Janar Emmanuel Undiendeye.
