Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, zai biya kudin karatun daliban da aka rikewa takardu a kasar Cyprus biyo bayan watsi da su da gwamnatin Ganduje tayi tsahon shekaru 5.
Gwamnan ya bayyana hakane a daren Lahadi bayan dawowarsa daga balaguron da yayi na makonni biyu zuwa kasashen ketare.
Gwamnan ya nuna takaicin sa kan yadda gwamnatin Ganduje ta ki biya musu Kudin karatu bayan sun kammala handa hakan yasa aka rike musu sakamako shekara da shekaru.
Ya ce sun dauki nauyin dalibai 500 domin yin Degree na biyu a kasar India kuma gwamnati zata dauke aiki da zarar sun dawo gida nan da kwanaki kadan.
Abba Kabir Yusuf, ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano ta dena yadda a biyawa yaro kudi yayi karatu a kasar waje sannan ya dawo yana yiwa wasu jihohi ko wata kasa aiki.
Ya ce mata 30 da gwamnati ta dauki nauyin karatun su na likitanci a kasar India wadanda suma da zarar sun dawo za a dauke su aiki domin su rinka kula da mata da kananan yara.
Wakilin mu na fadar gwamnatin Kano Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito cewa Gwamnan na Kano ya ce ya ziyarci kamfanin da yake gina tashar samar da wutar lantarki a madatsun ruwa na Tiga da Chalawa kuma kwanannan za’a ayi bikin bude kamfanin samar da wutar lantarki na Tiga.
Abba Kabir ya kuma ce sunyi yarjejeniya dasu zasu kammala na tashar samar da lantarki ta Chalawa dake Karaye.