Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano (KSPHCMB) ta musanta labarin bullar sabuwar cutar polio a Kano.
Shugaban hukumar Farfesa Salisu Ahmad ne ya bayyana Haka a a hirarsa da Primier Rado ranar Alhamis.
“Yanzu haka a nan jihar an dakile Polio duk a shekarar nan… ruwan da yake gurbace ne da aka yi wa gwaji aka tabbatar da cuta a ciki wanda kuma yara biyu ne kadai suka kamu da ciwon amma ba polio bane”. In ji shi.
Farfesa Salisu Ahmad Ya kuma tabbatar da cewa yaran da ake cewa sun kamu da polio ba polio bane makamanciyar cutar ce amma ba ta da hatsari.
Ya kuma tabbatar da cewa duk labaran dake yawo na yaran an dauki mataki an magance cutukan nasu, wanda yanzu haka sun warke kuma babu wani sabon raahoto dangane da irin wannan ciwo.
Ya kuma shawarci alumma dasu dinga yin rigakafin polio domin kariya daga cutuka.
