
Ƙungiyar Fafutukar Yaƙi Da Cin hanci Da Daidaito A Aikin Gwamnati (SERAP) ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya umarci Ministan Abuja Nyesom Wike ya janye barazanar rufe ofisoshin jakadancin ƙasashen waje 34 a Abuja bisa zargin kin biyan harajin kudin kasa.
A wata sanarwa da SERAP ta fitar a shafinta na X, ƙungiyar ta yi gargaɗi cewa barin Wike ya ɗauki matakin zai saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma yarjeniyar hulɗar diflomasiyya.
Martanin ƙungiyar na zuwa ne bayan da Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya FCTA ta bayyana cewa ana bin ofisoshin jakadanci 34 kuɗin harajin kasa tun shekarar 2014.
A ranar 26 ga watan Mayu ne Wike ya ba da umarnin ɗaukar mataki kan gine-gine 4,794 waɗanda ba su biya kuɗin haya ba ciki da ofisoshin jakadancin kasashe 34.
Ofisoshin jakadanci da abin ya shafa sun haɗa da na Ghana da Thailand da Equatorial Guinea da Côte d’Ivoire da Rasha da Philippines da Netherlands da Turkiyya da Guinea da Ireland da Uganda da Iraqi da Zambiya da Tanzaniya da Jamus da Kongo da Venezuela da Koriya da kuma Trinidad da Tobago.
Sauran sun haɗa da Masar da Chadi da Indiya da Sudan da Kenya da Zimbabwe da Ethiopia da Indonesiya da Tarayyar Turai da Switzerland da Saudiyya da China da kuma Afirka ta Kudu.
Hukumar ta FCTA ta kuma ce, ofisoshin jakadanci da abin ya shafa za su biya kuɗin tara da ya kai naira miliyan biyu ko uku kowannensu.