Kungiyar Kare Hakkokin Jama’a da Tabbatar da Daidaito ta SERAP da Kungiyar Editocin Najeriya (NGE) sun bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta gaggauta daina amfani da dokar laifukan yanar gizo wato Cybercrimes Act domin cin zarafin yan jarida.
Haka kuma kungiyoyin sun bukaci a sako wadanda ake tsare da su a fadin kasar nan karkashin wannan doka.
Kungiyoyin sun bayyana cewa, amfani da dokar laifukan yanar gizo wajen tsare mutane da ke bayyana ra’ayoyinsu cikin lumana na aikawa da sako mai karfi ga ‘yan Najeriya cewa ba za a ba da fifiko ga hakkokin dan Adam a mulkin Tinubu ba.
A cewar kungiyoyin amfani da dokoki da ba su da daidaito da kundin tsarin mulki da kuma ka’idojin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa — kamar dokar laifukan yanar gizo — yana ruguje dimokuradiyya da doka a Najeriya.
