Masarautar Saudiyya ta sanar da sabbin dokoki da ƙa’idojin lafiya da za su zama wajibi ga duk mahajjata da ke shirin gudanar da aikin Hajji a shekarar 2026.
Ma’aikatar Lafiyar Saudiyya ce ta fitar da sanarwar, inda ta umarci duk ƙasashen da ke tura mahajjata ciki har da Najeriya su tabbatar cewa duk masu niyyar zuwa aikin suna cikin koshin lafiya, tare da cikakkiyar shaidar gwajin lafiya.
A cewar ƙa’idojin, ba a yarda da mutane masu fama da matsanancin ciwon zuciya, hanta ko koda, ciwon hauka, matsalolin kwakwalwa, masu ɗauke da cututtuka masu yaduwa, ko mata masu juna biyu da ke cikin haɗari, su halarci aikin Hajji ba.
Daga cikin alluran da aka wajabta akwai:
Cikakken rigakafin COVID-19 tsakanin 2021 zuwa 2025 kafin tafiya.
Allurar sanƙarau aƙalla kwanaki 10 zuwa shekaru 5 kafin shiga ƙasar Saudiyya.
Ga ’yan Najeriya kuwa, sai an ƙara da allurar Polio (IPV ko bOPV/novel OPV2) aƙalla makonni 4 kafin tafiya.