
Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun hana Sheikh Ahmad Gumi shiga ƙasar domin gudanar da aikin hajjin bana.
Sheikh Gumi wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamnatin Saudiyya bayan ta ba shi bizar shiga ƙasar domin aikin Hajji amma kuma da isarsa kasar sai ta hana shiga Madina domin fara aikin ibada ba.
BBC ta rawaito cewa, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi na cikin tawagar malaman da Hukumar Aikin Hajjin Najeriya – NAHCON ta ɗauki nauyi domin zuwa aikin ibada a Saudiyya.
Gumi ya isa Madina ne tare da sauran malamai a ranar Asabar ne da misalin karfe 10:30 na dare a cikin jirgin sama na kamfani Umza Air, amma da isarsu filin jirgin sama na birnin sai jami’an hukumar shige da fice na Saudiyya suka hana malamin shiga cikin ƙasar.
Bayanai sun nuna cewa a yanzu haka Sheikh Gumi ya koma Najeriya domin ci gaba da harkokinsa na yau da kullum musamman karantarwa.