Ƙasashen Saudiyya da Qatar sun rattaba hannu kan yarjejeniya domin fara aikin gina dogo wanda zai ba da damar zirga-zirgar fasinja tsakanin manyan biranen ƙasashen biyu.
A cewar kafar yada labarai ta gwamnatin Saudiyya, jirgin ƙasan zai iya yin gudun sama da kilomita 300 a sa’a ɗaya, inda fasinjoji za su isa Riyadh daga Doha ko daga Doha zuwa Riyadh cikin sa’a biyu kacal.
Kamfanonin da za su gudanar da aikin sun bayyana cewa aikin zai ɗauki kimanin shekara shida kafin a kammala shi.
Ana ganin wannan mataki wani muhimmin ci gaba ne da zai ƙara ɗaure alaƙar Saudiyya da Qatar, musamman bayan takun-saƙa da ya faru a baya.
A shekarar 2017, dangantakar ƙasashen biyu ta yi tsami, bayan Saudiyya ta zargi Qatar da kusanci da Iran da kuma marawa wasu ƙungiyoyi masu ra’ayin tsattsauran addini baya.
