
Gwamnatin Saudiyya ta amince a yi jana’iza tare da binne gawar attajirin ɗan kasuwar nan na Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, a ƙasar.
Babban sakataren marigayin, Mustapha Abdullahi Junaid ya ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’iza tare da binne gawar marigayin a garin Madina.
A wani saƙo da Mustapha ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa, “AlhamdulilLah an samu amincewar (hukumomi).
“Za a ɗauki Aminu Alhassan Ɗantata daga Abu Dhabi zuwa birnin Madina.
Za kuma a yi jana’izarsa gobe Litinin da safe in sha Allah.” in ji shi.
A ranar Asabar ne shahararren ɗankasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya.
A shekarar Hijira (ta Musulunci) kuma, ya rasu yana da shekara 97, kamar yadda sakatarensa Mustapha Abdullahi ya bayyana.
Hamshaƙin attajirin ya rasu ne a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da jinya, kamar yadda wani ɗansa ya bayyana
Bayanai sun nuna cewa marigayin ya sha bayyana sha’awarsa cewa “Allah ka kashe ni a wannan gari” a duk lokacin da ya ziyarci garin Madina da ke Saudiyya.
Wannan karon farko a tarihi da aka yi shgar da gawar wani da dana dan kasar ba zuwa Saudiyya a kuma binne a can.