
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya fito daga fadarsa da misalin ƙarfe takwas na safe domin gudanar da Hawan Fanisau, daya daga cikin muhimman al’adun masarautar Kano.
Kamar yadda ya saba a hawan Daushe da Nasarawa, Sarkin ya fito ta Kofar Kwaru, inda ya bi ta titin Soron Dinki, ya gangara Makwarari, Gabari, Koki, Kofar Mazugal, sannan ya dangana da titin Hajji Camp zuwa Fanisau.
Sarkin ya bayyana cikin wata budaddiyar mota ta alfarma, tare da rakiyar hakimai, fadawa, da makada, waɗanda suka kayatar da zagayen da kida da al’adun sarauta.
Bayan isarsa Fanisau, Sarkin zai fara karɓar gaisuwar hakimai da sauran manyan masarauta.
Wakilinmu na masarauta, Khalil Ibrahim Yaro, ya rawaito cewa ɗaruruwan al’umma sun fito domin kallon mai martaba, wanda ke cike da kasaita da daraja ta sarauta.