Aminu Abdullahi Ibrahim
Mataimakin majalisar dattawa Sanata Barau Jibril, ya yi ban kwana da dalibai 70 maza da mata da ya dauki nauyinsu domin yin karatun Digiri na biyu a kasar Indiya.
Daliban da aka tura sun fito daga kananan hukumomi daban daban na jihar Kano, inda zasu yi digiri na biyu a bangarorin kimiya da fasaha.
Da yake jawabi yayin ban kwana da daliban a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, a yammacin asabar din nan, Sanata Barau Jibril ya ce yankin arewacin kasar nan na da rauni wajen ilimantar da matasa duk da arzikin da Allah ya yiwa yankin.
Ya kara da cewa da zarar daliban sun kammala karatu zasu sake tallafa musu ta yadda zasu kafa kamfanoni domin cigaban rayuwar su da al’umma baki daya.
Ya ce karkashin jagorancin sa ya samar da aikace aikace na cigaban al’umma a jihar Kano da kasa baki daya.
A cewarsa yanzu zasu maida hankali wajen ilimantar da matasan Arewa ta yadda zasu yi fice a tsakanin takwarorin su.
Barau Jibril, ya ja hankalin daliban da su mayar da hankali wajen yin karatu tare da zama jakadu nagari a inda zasu tsinci kansu.