Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga ’yan kasuwar da gobar Singa ta shafa.
Sanatan ya sanar da hakan ne a ranar Lahadi bayan ya ziyarci kasuwar.
“Wannan gobara da dimbin asarar da aka yi ta shafe mu baki daya. Hasali ma, ta shafi daukacin al’ummar Kano da ma kasa baki daya.
“Kasuwanci shi ne kashin bayan tattalin arzikin Kano, don haka wannan lamari ya taba mu kwarai da gaske,” in ji shi.
Sanatan ya kuma yi alkawarin samar da na’urorin zamani na shawo kan gobara a cikin kasuwar.
Shugaban kasuwar Alhaji Junaidu Zakari, a jawabinsa ya gode wa Barau bisa ziyarar da kuma tallafin kudi da ya bayar, yana mai cewa ‘yan kasuwar na alfahari da samun irin sanatan a Kano.
“Muna kuma godiya da duk irin goyon bayan da kake ba mu. Ka yi mana abubuwa da dama. Mun gode.” In shugaban.
Daruruwan ’yan kasuwar ne suka tarbi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijan a yayin ziyarar.
