
Tsohon shugaban rundnar tsaro ta Sibil Difens Abdullahi Gana Muhammad Mai ritaya ya ce, samar da Dakarun Kula Da Gandun Daji, da shugaba Tinubu ya yi zai kawo ƙarshen matsalar ‘yan ta’addan da suka addabi sassan kasar.
Gana ya kuma ce, samar da dakarun zai taka muhimmiyar rawa wajen yaki da ‘yan ta’addan da ma sauran bata garin da suke samun mafaka a dazuka, wajen gudanar da muggan ayyukan su na cutar da al’ummar da kasar gaba daya.
Shugaban hukumar tsaron ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da manema labarai a Abuja.
Abdullahi Gana ya ja hankalin al’umma da suka zage damtse wajen taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri domin kawar da ayyukan batagari. A ƙarshe ya yi fatan wadanda aka dorawa nauyin za su yi dukkan mai yiwuwa wajen magance matsalar tsaron da ta addabi sassan Najeriya, ta hanyar amfani da aikin nasu wanda