Sama da mutane 500,000 ne suka yi rijistar shiga jam’iyyar ADC cikin kwanaki hudu bayan Hukumar Zabe ta Kasa, INEC ta bayyana cewa jam’iyyar na fuskantar takaddamar shugabanci.
wannan na cikin bayanin da Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar na ƙasa, Malam Bolaji Abdullahi ya fitar.
Ya ce adadin sabbin mambobin ya karu ne tsakanin karfe 7:00 na yammacin ranar 1 ga Afrilu 2026, lokacin da INEC ta fitar da sanarwarta, zuwa karfe 5:00 na yammacin Lahadi 5 ga Afrilu 2026.
Ya kara da cewa wannan ci gaba na nuna yadda jama’a ke ci gaba da shiga jam’iyyar duk da kalubalen da ake danganta mata.
