Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa ta ba da umarni ga mambobinta da su dakatar da tura gas da kuma ɗanyen man fetur zuwa Matatar Fetur ta Dangote.
Wannan mataki ya samo asali ne daga rikicin da ya taso kan korar ma’aikatan kwamfanin na Dangote da suka shiga ƙungiyar.
Sakataren kungiyar Mr. Lumumba Okugbawa, ya bayyana cewa shugabancin masana’antar na zaluntar ma’aikatan saboda sun yi amfani da yancin da suke dashi wajan shiga ƙungiya da kundin tsarin mulki ya ba su.
Ƙungiyar ta yi ƙarar cewa akwai rashin kayan kariya da rashin kulawa da walwala da wariyar albashi da kuma rinjayen ƙwararrun yan kasashen wajan a manyan mukamai.
Sai dai masana’antar ta Dangote ta musanta zargin, tana cewa sauye-sauyen da aka yi na cikin gida ne domin inganta aiki, sannan ma’aikatan Najeriya sama da 3,000 na ci gaba da aiki a wajen.
Kungiyar ta yi gargaɗi cewa idan ba a warware rikicin ba, hakan na iya barazana ga tsarin samar da makamashi da tsaron tattalin arzikin ƙasa